Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya halarci zaman kotun sauraran kararrakin zabe a yau Talata 1 ga watan Agusta a Abuja. Atiku zai karanto tuhumarsa ta karshe da suka hada da zargin safarar kwaya na Shugaba Bola Tinubu .
Bayan karanto dukkan zarge-zargen da dama suna gaban kotun, akwai yiyuwar kotun ta sake saka ranar ci gaba da sauraran karar ko kuma ta yi watsi da karar.
Korafe-korafen sun hada da mallakar takardun kasancewa dan kasashe biyu da ke haramta masa zama shugaban Najeriya.
Mallakar shaidan kasancewa dan kasashe biyu ya sabawa dokar zabe da aka mata gyaran fuska a shekarar 2022. Ana zargin Shugaba Bola Tinubu da mallakar takardan shaidan zama dan kasar Guinea da ke Nahiyar Afirka.
Bayan zarge-zarge akan safarar kwayoyi da ake a kansa, akwai zargin tafka magudin zabe da aka gudanar a watan Fabrairu na wannan shekara.