Kano: ‘Yan sanda sun kama matar da ta kashe mijinta

Police badge

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama matar nan da ake zargi da kashe mijinta a ranar Talata, 6 ga watan Mayu, 2025, da misalin karfe 12:35 na safe.

SolaceBase ta ruwaito cewa wacce ake zargin mai suna Saudat Jibril, ‘yar shekara 18 a unguwar Farawa, ta yanka mijin nata mai suna Salisu Idris dan shekara 30 a makogwaro da wuka mai kaifi.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce da samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gaggauta tura tawagar ‘yan sanda zuwa wurin.

“An garzaya da wanda aka kashe zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsa,” in ji sanarwar.

Karin karatu: Kano: ‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi da laifin fashi da makami da kisan kai

‘’An kama wadda ake zargin kuma a halin yanzu tana tsare a sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda (CID), sashe na kisan kai, kuma za a gurfanar da ita a gaban kotu bisa laifin aikata laifin kisa.

‘’Kwamishanan ‘yan sandan ya yi gargadin cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’i na tashin hankali ko aikata laifuka a jihar ba, ya kuma ba jama’a tabbacin gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da an yi adalci.

‘’Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tana kira ga jama’a da su sanya ido tare da kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta layukan waya kamar haka: 08032419754, 08123821575, da 09029292926.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here