Jamus zata maido wa da Najeriya kayan tarihi 1,130 da aka wawashe – Minista

Benin Africa Art Western Museums
Benin Africa Art Western Museums

Ministan labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya ce Najeriya ta kulla yarjejeniya da kasar Jamus akokarin maido da kayayyakin tarihi na kasar Benin sama da 1,130 da aka sace zuwa kasar.

Mohammed ya bayyana hakan ne a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a birnin Washington DC ranar Talata, bayan da wasu gidajen tarihi guda uku da ke Amurka suka mayar da kayayyakin tarihi guda 31 zuwa Najeriya.

Ya yabawa gwamnatin Jamus kan wannan yunƙuri inda ya ƙara da cewa Najeriya na samun tagomashi daga ƙasashen Faransa da Mexico na maido da wasu kayan tarihi da aka sace.

A shekara ta 1897 lokacin da Birtaniyya ta kai wa Benin hari, an kona fadar sarki tare da wawashe dukiyar kasar, sannan aka yi wa oba (mai mulki) gudun hijira.

Birtaniyya ta kwace duk wasu dukiyar sarauta, inda ta baiwa wasu jami’ai guda daya sannan aka yi gwanjon su a Landan.

An kiyasta abubuwa 3,000 daga ƙarshe sun shiga gidajen tarihi masu tarin yawa masu zaman kansu a duniya.

Ministan ya ce duniya ta ga cewa abu ne da ya dace a mayar da kayayyakin ga masu su, yana mai cewa ba batun doka ba ne kamar yadda gwamnatin Burtaniya ta yi iƙirari.

A cewarsa Najeriya na shirin kulla yarjejeniya da gwamnatin Birtaniya a ranar 28 ga watan Nuwamba domin mayar da wasu kayayyakin tarihi kusan 86 daga gidajen tarihi daban-daban a kasar ta Burtaniya.

Ministan ya shaida wa kamfanin dillacin labaran najeriya cewa yakin da gwamnati mai ci ke yi na maido da kayayyakin tarihi na Najeriya da aka wawashebdaga sassan duniya, na samun sakamako mai kyau.

Ya ce a watan Janairu, Najeriya da Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kadarorin al’adu na kasashen biyu domin hana shigo da wasu kayayyakin tarihi na Najeriya ba bisa ka’ida ba cikin Amurka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here