Gamayyar jam’iy canyun siyasa ta [CUPP] ta yi zargin cewa akwai alamun yunkuri da ake na tsige Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa Farfesa Mahmood Yakubu a yunkurin kawo cikas a zaben 2023.
Shugaban CUPP na kasa Mista Ikenga Ugochinyere ya bayyana haka a madadin jam’iyyun adawa, yayin wani taron manema labarai.
Ya ce kungiyar ta kuma bankado wasu sabbin tsare-tsare da akeyi na hana amfani da tsarin tantance masu kada kuri’a da na’urar BVAS a zaben.
Rahotanni sun ce ana kokarin dakatar da watsa sakamakon zabe azamanan ce kwmar yadda hukumar ta tsara wanda hakan zai yi maganin magudi a rumfunan zabe.
Gamayyar kungiyoyin wadanda suka kunshi mafi yawan jam’iyyun siyasa na adawa da suka hada da jam’iyyar PDP da kuma Labour Party.
Ugochinyere ya kuma yi zargin cewa wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki a yankin Kudu maso Gabas na jam’iyyar ne ke jagorantar wannan yunkuri.
A baya dai gamayyar kungiyoyin sun zargi gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma da tafka magudi a cikin rajistar masu zabe a jihar, lamarin da ya sa INEC ta mayar da martani kan wannan tirka tirka.
Kungiyar ta bada misali da kame jami’an hukumar zabe a jihar Imo da hukumar DSS ta tsare sama da mako guda ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ba, a wani bangare na shirin tursasa alkalan zabe da kuma tsige shugaban kamar yadda aka tsige Alkalin Alkalan Najeriya daga mukaminsa kafin babban zaben 2019.
Cikakkun rahotanni na nan tafe gaba kadan…










































