An rantsar da Alkalin Alkalan Najeriya Olukayode Ariwoola

FB IMG 16655801609212686
FB IMG 16655801609212686

An rantsar da Alkalin Alkalan Najeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a Abuja, babban birnin kasar.

Babban jojin na Najeriya ya sha rantsuwa ne a fadar shugaban Najeriya ranar Laraba, wata hudu bayan ya hau kan mukamin sakamakon murabus din Mai shari’a Ibrahim Tanko.

Mai shari’a Tankon ya yi murabus ne bisa dalili na rashin lafiya.

Wani sako da fadar shugaban kasar ta wallafa a shafin Tuwita ya nuna cewa Alkalin Alkalan Najeriyar ya sha rantsuwa ne da safiyar yau.

An haife shi ne a watan Agustan shekarar 1954, kuma ya yi alkalanci a Kotun Daukaka Kara ta Najeriya, kafin ya samu daukaka zuwa Kotun Kolin kasar.

Ariwoola Musulmi ne ɗan asalin jihar Oyo, kuma ya shafe kusan shekara 11 a matsayin ɗaya daga cikin manyan alƙalan Kotun Ƙolin, bayan shigarsa cikinta a watan Nuwamban 2011.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here