Jam’iyyu 5 sun nuna goyon bayan su ga Atiku Abubakar

atiku5
atiku5

Biyar daga cikin jam’iyyun siyasa 18 a Najeriya sun amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, mako guda kacal gabanin babban zaben kasar.

Jam’iyyun siyasar biyar sun bayyana hakan ne a babban taron gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a dandalin Mahmud Ribadu, da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Daga cikin jqmiyyun sun hada da jqmiyyar APM, Allied Peoples Movement, African Democratic Congress, National Rescue Movement, Action Alliance da Action Peoples Party.

Shugaban jam’iyyar APM na kasa Yusuf Dantalle ne ya bayyana hakan a madadin jam’iyyun.

A ranar Juma’a ne shugaban jam’iyyar APM na kasa ya amince da takarar Atiku a madadin ‘yar takarar shugaban kasa mace daya tilo a jam’iyyar APM, a zaben shugaban kasa na 2023, Chichi Ojei.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here