PDP za ta zama tarihi idan Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa a 2027 – Bode George

Bode George 750x430

Wani jigo a jam’iyyar PDP, Cif Bode George, ya ce jam’iyyar PDP za ta ruguje idan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa a 2027.

George, mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BoT), ya yi magana a ranar Litinin lokacin da yake hira a cikin shirin Siyasa A Yau, na gidan Talabijin na Channels.

Abubakar wanda shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya sha kaye a hannun Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a shekarar 2023, wasu masu ruwa da tsaki, ciki har da kungiyar gwamnoni biyar, sun bukaci a ware tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudu bisa tsarin karba-karba a kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Karanta: Dalilin da ya sa muka ziyarci Buhari a Kaduna – Atiku

Rikicin ya kara tsananta saboda tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari dan Arewa ne daga Katsina yana kammala wa’adin mulkin sa na biyu.

Wasu ‘yan jam’iyyar sun janye goyon bayansu ga Atiku bayan ya lashe tikitin takarar shugaban kasa.

Sai dai tattaunawa a baya-bayan nan game da kafa kawance don kalubalantar jam’iyyar APC na kara samun karbuwa gabanin zaben 2027.

‘Yan siyasan adawa dai na gudanar da tarurrukan dabarun kafa kawance, inda tsohon mataimakin shugaban kasar ya taka rawar gani.

Sai dai kuma a wani yanayi na ci gaba da aka samu a ranar Litinin, gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar PDP sun yi watsi da yiwuwar hadewa ko hadaka da wata jam’iyyar siyasa gabanin zaben 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here