Ana baiwa fursunoni abincin safe, rana da na dare kowace rana- hukumar NCoS

NCos jail break 750x430

Hukumar da ke kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta kasa NCoS, ta yi watsi da rahotannin da ke cewa fursunonin na fama da rashin abinci da yunwa a cibiyoyin da ake tsare da su a fadin kasar nan.

Da yake mayar da martani kan zargin, a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Talata a Abuja, jami’in hulda da jama’a na Hukumar (SPRO), Abubakar Umar, ya ce rahotannin ba gaskiya ne kuma basu da inganci.

Ya yi bayanin cewa Gwamnatin tarayya na yin tanadin kasafin kudi na musamman duk shekara domin ciyar da fursunoni, kuma ana yin amfani da kudaden ne cikin adalci a karkashin kulawa da ka’idoji.

Ya bayyana cewa kowane fursuna yana da hakkin cin abinci sau uku a kullum – karin kumallo, abincin rana, da abincin dare – kamar yadda aka tsara a cikin ka’idojin aiki na hukumr.

Karin karatu: PDP za ta zama tarihi idan Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa a 2027 – Bode George

“Zargin cewa fursunonin na mutuwa saboda yunwa ba gaskiya ba ne, babu wani labari a cikin cibiyoyin da muke tsare da su cewa fursunonin na fama da yunwa ko kuma suna mutuwa saboda rashin isasshen abinci.”

A cewarsa, gwamnatin shugaba Bola Tinubu a halin yanzu ta inganta kudaden da take baiwa hukumar don jindadin fursunoni da ababen more rayuwa.

Ya kara da cewa ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya kuma nuna jajircewarsa wajen gyara tsarin hukumar ta kowanne fuska.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here