Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence (CUSTECH) da ke Osara a jihar Kogi ta karrama Usman Yahaya Kansila, shugaban kamfanin UYK Consortium, da Digirin girmamawa a wani bikin yaye dalibai da aka gudanar a karshen mako.
A wurin bikin, shugaban jami’ar, Abdulrahman Asipita Salawu, ya bayyana cewa majalisar jami’ar da majalisar gudanarwa sun amince da wannan karramawa bisa la’akari da gagarumar gudunmawar da Kansila yake bayarwa wajen ci gaban ilimi a jihar Kogi da kuma sassan Najeriya.
Ya ce wannan karramawa na nuna jajircewar jami’ar wajen girmama shugabanni da suka sadaukar da kansu don bunkasa harkar ilimi, tare da bayyana cewa ana sa ran wannan yabo zai kara karfafa hadin gwiwa da shirye-shiryen da suka shafi inganta ilimi a jihar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa manyan baki da suka raka Kansila wurin bikin sun hada da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Hafiz Abubakar; Ahmad Nakura; Mahmoud Nabegu; Usman Lawan; Muhammad Yakubu Auna; da Ahmad Aliyu Yakasai, tare da wasu.
An haifi Kansila a ranar 13 ga Oktoba, 1968, kuma ya yi karatunsa na firamare da sakandare a Kano, kafin ya ci gaba zuwa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano, inda ya samu takardar OND da HND a fannin kudi.
A shekarar 2021 jami’ar koyar da harkokin noma ta Michael Okpara ta karrama shi da Digirin girmamawa saboda gudunmawar da yake bayarwa ga al’umma.
Kansila ya fara aikinsa a ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ta jihar Kano na tsawon shekaru takwas, kafin ya kafa kamfanin UYK Nigeria Limited a 1998.
Kamfanin ya bunƙasa sosai cikin shekaru 25, inda ya zamo rukuni mai reshe-reshe kamar UYK Real Estate, UYK Industries da UYK Resources and Technologies, tare da daukar ma’aikata sama da guda 500.
Kansila ya kafa gidauniyar Yahaya Kansila domin tallafa wa al’umma, wadda ke daukar nauyin dalibai daga matakin firamare zuwa jami’a, ciki har da tallafin kammala karatu, tarukan ilmantarwa, da kuma shirye-shiryen bunkasa kwarewa.
Gidauniyar tana daukar nauyin kusan dalibai 1,600 a duk shekara tare da aiwatar da ayyukan gina makarantu da gyare-gyare a Kano, kana tana daukar nauyin gina dakunan kwana na mata a jami’ar Bayero mai darajar fiye da naira miliyan 700.
Kansila memba ne na cibiyar gudanar da harkokin gudanarwa ta Najeriya (NIM) da kungiyar injiniyoyi ta Najeriya (NSE).
Ya samu lambobin yabo iri-iri daga kungiyoyin kwararru, kana kuma ya yi fice wajen tafiya da gudanar da harkokin kasuwanci.
Yana da mata da ‘ya’ya biyar.













































