Gwamnan Kano ya musanta jita-jitar barazanar tsaro a jihar 

WhatsApp Image 2025 12 01 at 07.43.15 750x430

Gwamnatin jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa tsaron jihar yana nan cikin aminci kuma babu wata barazana da za ta tayar da hankalin jama’a.

Wannan bayanin ya fito ne daga sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan zaman majalisar tsaro ta jihar da aka yi ranar Lahadi tare da shugabannin hukumomin tsaro.

Gwamnatin ta bayyana cewa binciken da aka gudanar bai nuna wata sahihiyar barazana ga zaman lafiya ba, duk da yaduwar labaran ƙarya da ke neman sanya tsoro da ɓata hankalin jama’a a cikin jihar.

Haka kuma gwamnati ta yi Allah-wadai da yadda ake yaɗa bayanan da ba su da tushe domin tayar da hankalin al’umma.

Karanta: Gwamnatin Kano ta ƙuduri aniyar ɗaukar mataki yayin da masu sana’ar Achaba da aka haramta suka sake bayyana

Duk da cewa jaridar Solacebase ta rawaito cewa fiye da mutane goma an sace su a wasu yankunan Kano tare da mutuwar akalla uku cikin makonni uku da suka gabata, gwamnati ta ce tana aiki tare da hukumomin leken asiri, jami’an tsaro, da Dattawan al’umma domin inganta tsaro a kowane yanki.

Sanarwar ta ce an tura jami’an tsaro zuwa wuraren da suka dace tare da sa ido a ko’ina domin tabbatar da hana duk wani abin da zai kawo tashin hankali.

Haka kuma kowane sashe na Kano yana cikin tsaro mai ƙarfi tare da kulawa ta musamman.

Gwamnati ta yi kira ga jama’a da su kasance masu natsuwa da kishin kasa, tare da yin taka tsantsan wajen amfani da kafafen sada zumunta.

Ta kuma gargadi masu yaɗa labaran ƙarya da su daina domin hakan na iya janyo hukunci.

Sanarwar ta shawarci mazauna jihar da su ci gaba da harkokin yau da kullum ba tare da wata fargaba ba domin Kano na cikin kwanciyar hankali da tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here