ICPC za ta gurfanar da wani Ɗan jarida na Kano bisa zargin almundahana

icpc hq fasad 750x430

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuffuka masu Alaƙa da su (ICPC) ta bayyana shirinta na gurfanar da wani mutum mai suna Alkazim Kabir, wanda aka fi sani da Abbati Kabiru Abuwa, wanda yake iƙirarin shi ɗan jarida ne a Kano, bisa zargin aikata zamba da ta kai kusan naira miliyan 14.

Bisa bayanan da hukumar ta samu, an samu korafe-korafe da dama daga mutane daban-daban suna zargin wanda ake tuhumar da aikata damfara ta yau da kullum, yin bogi, da kuma kwaikwayon jami’an gwamnati domin yaudarar jama’a.

Binciken hukumar ICPC ya gano cewa wanda ake zargin yana kwaikwayon fitattun mutane ciki har da hadiman shugaban ƙasa da mataimakinsa, da kuma ‘yan majalisar tarayya domin karɓar kuɗi daga mutane bisa zamba.

A cikin wani lamari da aka gano, ya karɓi dala $3,300 da Riyal 1,620 na ƙasar Saudiyya daga wasu mutane biyu, yana mai ikirarin cewa hadimi ne na shugaban ƙasa da mataimakinsa.

Karanta: Ba Ganduje ko Gwamnatin Kano ke da hannun jari a tashar Tsandauri ta Dala ba – Hukumar Gudanarwa

Haka kuma bincike ya nuna cewa Alkazim Kabir ya kware wajen karɓar kuɗi da kaya ta hanyar yaudara, musamman a lokutan da suka shafi tafiyar ibada zuwa ƙasashen waje.

A wani lokaci a ƙasar Saudiyya, an ce ya karɓi Riyal 11,000 daga wani abokin tafiya sannan ya aika masa da takardar bogi ta banki a matsayin hujjar biyan kuɗin.

Haka kuma ya tura takardar canja kuɗi ta ƙarya ta naira miliyan 3.2 ga wani dillalin tafiye-tafiye da ya shirya masa tikiti da otel da jirgin ƙasa.

Hukumar ICPC ta tabbatar da cewa an riga an shigar da ƙarar a gaban kotu, kuma ana jiran a bai wa wata babbar kotu shari’ar domin fara gurfanar da wanda ake tuhumar bisa waɗannan zarge-zarge.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here