HOTONA: WOFAN ta kaddamar da babban ofishi na zamani a Abuja

WhatsApp Image 2024 11 13 at 14.40.48 750x430

Kungiyar WOFAN mai hedikwata a Kano, arewa maso yammacin Najeriya, ta kaddamar da wani sabon Ofishinta a gundumar Jabi dake babban birnin tarayya Abuja.

SolaceBase ta rahoto cewa WOFAN kungiya ce mai zaman kanta ta Najeriya da aka kafa don inganta tattalin arziki, zamantakewa, taimakawa mata dake karkara, da kuma matasa domin su samin rayuwa mai kyau a Najeriya.

WhatsApp Image 2024 11 13 at 14.48.43 645x430

Da take kaddamar da ofishin, a ranar Talata, Daraktar WOFAN-ICON2, Dakta Salamatu Garba ta ce kungiyar na fadada kuma a halin yanzu tana gudanar da ayyukanta a jihohi goma na arewa da suka hada da arewa maso yamma, arewa maso gabas da arewa ta tsakiya.

“WOFAN na da ofisoshi guda biyu a Abuja, wato a Maitama da Garki amma mun yi aiki a can na dan lokaci a matsayin gurin haya, wannan shi ne ginin mu na dindindin, inji Dokta Garba.

A cewarta, harabar makarantar ta WOFAN Comprehensive School ce kuma za ta kasance ofishin gudanarwa na WOFAN kamar yadda tsarin Kano yake.

WhatsApp Image 2024 11 13 at 14.50.54 1 645x430

‘’Kun san cewa WOFAN tana da bangarori da dama, kamar makarantar, WOFAN Tauraruwa Rice, WOFAN Center da sauransu, don haka ofishin nan na Abuja zai mana amfani sosai.”

‘’Yanzu haka, WOFAN ta fitar da injina don inganta ayyukan noma mata manoma da nakasassu a kananan hukumomin FCT, Benue da Jihar Nasarawa.

WhatsApp Image 2024 11 13 at 14.44.31 645x430

”Wannan ita ce shekara ta uku da fara aiki a Abuja kuma muna shirin fadada ayyukan bada tallafi ga al’ummomin karkara na Abuja”.

kaddamar da ofishin ya samu halartan ma’aikatan WOFAN daga Kano, Bauchi, Gombe Adamawa, Abuja da sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here