HOTONA: Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yiwa dansa da aka karawa matsayi zuwa Birgediya Janar ado

Ex President Olusegun Obasanjo and son Brig. Gen. Adeboye Obasanjo
Ex President Olusegun Obasanjo and son Brig. Gen. Adeboye Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yiwa dansa Adeboye Obasanjo ado da mukamin Birgediya Janar a rundunar sojin Najeriya.

An gudanar da taron ne a hedikwatar Injiniyoyin Sojojin Najeriya dake Legas, ranar Laraba

Solacebase ta ruwaito cewa bikin ado ya biyo bayan karin girma da dan ya samu daga mukamin Kanar zuwa Birgediya Janar a rundunar sojin Najeriya.

Bikin dai ya kasance mai tarihi ga tsohon shugaban kasa Obasanjo, wanda shima ya kasance cikin rundunar Injiniyoyin sojojin Najeriya a lokacin yana soja. Yanzu kumaga Ɗansa shima ya kasance cikin rundunar.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumomin sojin kasar sun bai wa tsohon shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunar sojin tarayyar Najeriya wata gata da ba kasafai ake yi ba, inda ya yi wa dansa ado da sabon karin girma da ya yi wa Birgediya Janar a hedikwatar Rundunar Injiniyoyin Sojojin Najeriya a sansanin Bonny, Legas.

Tsohon shugaban kasar ya samu rakiyar Towulade na masarautar Akinale ta Egbaland, Oba Olufemi Ogunleye, wajen bikin.

Sabon Birgediya Janar OA Obasanjo yana da digiri biyu (Master Degree) da sauran shedun karatu dana kwarewar aiki.

Ya kuma halarci kwasa-kwasai a Najeriya da kasashen waje. Ya kuma yi aiki a sassa da sassa daban-daban na sojojin Najeriya, inda ya rike mukamai daban-daban.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here