Gwamnatin jihar Katsina ta yi bayani kan dalilan da suka sa take shirin taimakawa wajen sakin mutane 70 da ake zargi da aikata laifukan fashi da makami, waɗanda a halin yanzu suke fuskantar shari’a a kotu.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafawa da faɗaɗa yarjejeniyar zaman lafiya da aka riga aka cimma tsakanin al’ummomin da matsalar tsaro ta shafa a ƙananan hukumomi 15 na jihar da kuma masu aikata laifukan da suka nuna nadama.
Gwamnatin ta jaddada cewa irin wannan dabara ana amfani da ita a ƙasashe daban-daban a lokutan rikici, inda ake ɗaukar matakan sulhu domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
Ta ƙara da cewa wannan yarjejeniya ta riga ta haifar da sakin aƙalla mutane 1,000 da aka sace a hare-hare daban-daban da aka kai a faɗin jihar.
A ranar 2 ga Janairu 2026, wata takarda ta fito fili wadda ta bayyana shirin gwamnatin jihar na ganin an saki waɗannan mutanen da ake zargi, waɗanda ke fuskantar shari’o’i a kan laifukan fashi da makami.
Takardar, wadda aka yi mata alamar sirri, Ma’aikatar Shari’a ta jihar ce ta fitar da ita zuwa ga Babban Alkalin Jihar Katsina, Mai shari’a Musa Abubakar.
Karanta: Kano: ‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi da laifin fashi da makami da kisan kai
A cikin takardar, Ma’aikatar Shari’a ta nemi sa hannun Kwamitin Kula da Aiwatar da Dokar Shari’ar Laifuka na Jihar Katsina domin taimakawa wajen sakin mutanen da ake tsare da su.
Daraktan Gurfanar da Masu Laifi na jihar, Abdur-Rahman Umar, ya sanya hannu a kan takardar, inda ya bayyana cewa Ma’aikatar Tsaron Ciki da Harkokin Gida ta tura jerin sunayen mutane 48 da ake zargi da laifukan fashi da makami zuwa ma’aikatar shari’a a matsayin wani sharadi na ci gaba da yarjejeniyar zaman lafiya.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da ake zargin suna fuskantar shari’a ne a gaban Kotun Tarayya, yayin da wasu kuma ke tsare suna jiran fara shari’a a kotunan majistare daban-daban a jihar.
Haka kuma, an miƙa wani jerin sunaye na ƙarin mutane kusan 22 da ke gaban manyan kotuna a faɗin jihar, domin a sake su a ƙarƙashin wannan tsari na sulhu.
Wannan buƙata ta haifar da martani daga lauyoyi, ƙungiyoyin farar hula da kuma jama’a, inda masu suka suka yi nuni da cewa sakin mutanen da ake zargi da manyan laifuka na iya raunana ikon doka, hana adalci ga waɗanda abin ya shafa, da kuma ƙarfafa ƙungiyoyin masu laifi.
Sai dai Kwamishinan Tsaron Ciki da Harkokin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa matakin yana da muhimmanci wajen ƙarfafa yarjejeniyoyin zaman lafiya da al’ummomi suka jagoranta da masu aikata laifukan da suka nuna nadama, tare da jaddada cewa an cimma nasarori masu yawa da suka haɗa da sakin kusan mutane 1,000 a ƙananan hukumomi daban-daban ta hanyar tattaunawa mai tsari.
Gwamnatin ta bayyana cewa buƙatar sakin mutanen tana cikin ikon doka na Kwamitin Kula da Aiwatar da Dokar Shari’ar Laifuka na Jihar Katsina ƙarƙashin sashe na 371(2) na Dokar Shari’ar Laifuka ta shekarar 2021.
A gefe guda, Kwamishinan Tsaron Ciki da Harkokin Gida na jihar, Dakta Nasiru Danmusa, ya ce babu wata doka da aka karya, yana mai ba duk wanda bai gamsu da matakin ba shawarar neman mafita ta hanyar doka.













































