Gwamnatin Kano ta samar da dokar kare muhalli don yaƙi da gurɓatar yanayi

WhatsApp Image 2025 04 09 at 00.45.10 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ɓullo da sabbin dokokin kare muhalli da nufin magance matsalar gurbatar muhalli a jihar.

Kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Dr. Dahir M. Hashim ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Talata, jim kadan bayan gabatar da dokokin ga sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, wanda ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shirin.

Hashim ya kara da cewa, “An kirkiro wadannan dokoki ne domin magance gurbatar muhalli, musamman batutuwan da suka shafi fitar da sinadarai masu cutarwa, zubar da shara barkatai musamman a kan tituna, da sako gurbataccen ruwa da masana’antu ke yi, da dai sauransu.”

SolaceBase ta ruwaito cewa Dr. Hashim ya kara bayyana cewa, tare da amincewar Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ma’aikatar za ta fara gudanar da gangamin wayar da kan jama’a na tsawon mako takwas.

Gangamin dai zai shafi daidaikun mutane domin wayar da kan jama’a game da mahimmancin tsafta da kula da muhalli.

Ya kara da cewa “In Allah ya yarda, za mu buga dokokin cikin harshen Hausa da Ingilishi a cikin mako guda domin jama’a su karanta su fahimce su.”

Kwamishinan ya bukaci mazauna jihar Kano su goyi bayan kokarin gwamnati na inganta tsaftar muhalli, wanda zai inganta lafiyar al’umma da kuma jin dadin jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here