Ganduje ya musanta yunkurin tuɓe Shekarau daga sarautar Sardauna

images
images

By Aminu Bala Madobi.

Gwamnatin Jihar Kano, ta musanta raɗe-raɗin yunkurin da ake cewa Gwamna Ganduje na yi na tuɓe tsohon gwamnan Kano kuma Sanata Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau daga sarautar Sardaunan Kano.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Gwamna Ganduje da Sanata Shekarau, suna zaman doya da manja a baya-bayannan biyo bayan zaɓukan shugabannin Jam’iyyar APC da kowanne tsagi ke iƙrarin samar da halastaccen shugaban Jam’iyyar.

Rahotonnin sun ce ɓangaren gwamnati da ke biyayya ga gwamna Ganduje ya fidda Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC yayin da tsagin Sanata Shekarau ya zaɓi Alhaji Ahmadu Haruna Danzago, lamarin da ke cigaba da dumama tsakanin bangaren biyu.

Idan za a iya tunawa, marigayi sarkin Kano  Alhaji Dakta Ado Bayero, ne ya naɗa Mallam Shekarau amatsayin Sardaunan Kano a shekarar 2007.

Rahotannin da ke cigaba da yawo na nuna cewa gwamna Ganduje na shirin tumɓuke sarautar Sardaunan ne domin ramako game da rashin biyayya da yake zargin Sanata Shekarau na yi masa.

Da yake mayar da martani, mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin masarautu Alhaji Tijjani Mai Lafiya Sanka ya ce, ba bu ƙamshin gaskiya cikin wannan zarge-zarge.

“Kun ga gwamna mutum ne mai kirki da Hakuri, Wanda ke saka wa da alheri idan an ɓata masa, kuma idan kun duba Malam Ibrahim Shekarau ya rasa makoma a siyasa amma a 2019 Ganduje ya janyo shi jika ya bashi takarar Sanata ba tare da ya bai wa kowa damar fitowa a takarar kujerar ba” Inji Sanka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here