Firaministar Birtaniya ta sauka daga muƙaminta

Prime Minister Liz Truss 750x430 1
Prime Minister Liz Truss 750x430 1

Firaministar Birtaniya Liz Truss ta sauka daga muƙaminta bayan kwana 45 da hawa kan mulki.

Ƴan majalisa na jam’iyyar Conservatives sun buƙace ta da ta ajiye mulki bayan da gwamnatin tata ta ci karo da matsaloli.

Ajiye muƙamin nata ya zo ne bayan da wata minista mai matuƙar muhimmanci ta ajiye aiki, yayin da ƴan majalisa na jam’iyyar Conservatives suka yi mata bore.

A watan Satumba ne aka zaɓi Truss a matsayin firaminista, sai dai kwarjininta ya yi ƙasa bayan soke wasu daga cikin tsare-tsaren da ta ɓullo da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here