‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 jihar Benue

1fe87bb49d666606
1fe87bb49d666606

‘Yan bindiga sun halaka mutum 23 ciki harda wani jami’in dan sanda sannan suka jikkata mutum 11 yayin da suka kai farmaki garin Gbeji da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benue.

Maharan sun kai mummunan harin ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba,kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Mai ba gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Lt Col. Paul Hembah (rtd), wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce dan sandan wanda ya ji mummunan rauni ya mutu ne a hanyar zuwa asibiti.

Da yake tabbatar da kashe-kashen, kwamishinan yan sandan jihar, CP Wale Abass, a wata hira ya ce makiyaya biyar sun mutu a harin tare da dan sandan.

Ya ce an tura tawagar yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro zuwa yankin don dawo da zaman lafiya.

Wani mazaunin garin wanda ya bayyana sunansa a matsayin Elder Iorngaem Kerepe ya ce baya ga mutanen da aka kashe maharan sun kona akalla gidaje 50. Ya ce tuni mazauna kauyen suka yi kaura daga gidajensu yana mai cewa har yanzu ba a ga wasu da dama ba.

“Na kadu da harin, duba ga cewar akwai jami’an sojoji a Kente, wani matsuguni a iyakar Benue-Taraba, kilomita 2 daga Gbeji, da kuma wata tashar bincike na sojoji a Gou, kilomita 3 daga Beji amma makiyaya dauke da makami suka kaddamar da hari tsawon awa daya ba tare da tangarda ba.”

Har ila yau da yake tabbatar da lamarin, shugaban yankin, Tyoumbur Kaatyo, ya bayyana harin a matsayin wanda bai dace ba yana mai cewa tuni aka ajiye gawarwaki wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa. Ya kuma ce an kwashi wadanda aka sassara zuwa wani asibitin gwamnati da ke Afia domin samun kulawar likitoci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here