Yan Sanda Sun Harbawa Matasa Barkonon Tsohuwa A Lekki Tollgate

57913310bbc9ec90
57913310bbc9ec90

Jami’an rundunar yan sandan Najeriya sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa matasan da ke bikin tunawa da zanga-zangar #EndSARS a Lekki tollgate. Jaridar TheCable ta rahoto cewa an shirya gangamin ne domin cikar shekaru biyu da gudanar da gangamin EndSARS

A safiyar yau Alhamis, 20 ga watan Oktoba ne matasa suka taru a yankin tollgate suna ta wake-wake yayin da suke rike da akwatin gawa don tunawa da lamarin da ya afku a ranar 20 ga watan Oktoban 2020.

Gangamin wanda aka yiwa lakabi da ‘tattakin lumana’ ya dauki sabon salo yayin da jami’an yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin fatattakar wadanda ke tattakin.

Kakakin yan sandan jihar Lagas, Benjamin Hundeyin, ya fada ma Channels TV cewa wasu daga cikin masu tattakin basu bi doka ba sannan sun dare saman tollgate. Ya ce:

“Babu bukatar aikata haka. Kuna tattaki, kawai ku yi tafiyarku. Amma sai wadannan mutanen suka tsaya a wajen sannan suka dare saman tollgate, sun zama masu hayaniya, suna barazanar karya doka da oda da ke kasa. “Ba za mu tsaya a nan muna kallonsu suna rashin da’a ba. Abu mafi sauki da za mu iya yi shine amfani da barkonon tsohuwa, duk wani abu baya ga barkonon tsohuwar zai zama mai cutarwa. “Ba a samu wanda ya ji rauni ba. Kawai aikinmu muka yi sannan muka fuskanci wadanda suka nuna rashin da’a.”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here