Tsohon ministan sifirin jiragen sama, Hadi Sirika ya bi sahun sauran ‘yan takarar neman kujerar sanatan Katsina da Arewa a Majalisar Dattawa.
Sirika ya bayyana aniyar ta shi ne a sakatariyar jam’iyyar APC a ranar Juma’a, a wani gangami da yayi zuwa sakatariyar tare da magoya baya.
Ya bayyana kansa a matsayin mutum bai gogewa da kuma ya cancanci ya wakilci yankin a majalisar kasa.
Sirika tsohon dan majalisar wakilai ne daga shekarar 2003 zuwa 2007 kafin a zabe shi a matsayin sanata a shekarar 2011.
Tsohon ministan yayi alkawarin girmama dokokin jam’iyyar kafin gudanar da zabukan fidda gwani. Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar APC za ta yi nasara a duk zabukan da za a gudanar a matakin jiha da kasa baki daya.
Ya kuma kaddamar da kungiyar Dikko Kalas da ya bayyana cewa zata maida hankali kacokan wajen zaburar da jama’a gida-gida a fadin jihar Katsina.
A shekarar 2023, ma’aikatar sifirin jiragen sama ta kaddamar da jirgin saman Najeriya (Nigeria Air) kwanaki uku kafin karewar wa’adin mulkin tsohon shugaban kasa Marigayi Muhammadu Buhari.
Sai dai kuma hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta gurfanar da Sirika a gaban koto bisa zargin baiwa ‘yan uwansa damarmaki na biliyoyin Nairori a lokacin da yake rike da mukamin ministan sifiri.a












































