Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta ceto wani yaro mai shekara biyu da aka sace, tare da kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifin, sannan ta kwato wani ɓangare na kuɗin fansa da aka biya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar a Kano.
Kiyawa ya bayyana cewa a ranar 19 ga watan Afrilu, wani mazaunin unguwar Gwammaja a ƙaramar hukumar Dala ya kai rahoton cewa an sace ɗansa Aliyu Muhammad mai shekara biyu a gaban gidansu daga hannun wasu mutane da ba a san su ba.
Ya ƙara da cewa daga baya waɗanda ake zargin sun tuntubi iyalan yaron inda suka nemi a biya su kuɗin fansa Naira Miliyan Ɗaya, wanda iyalan suka biya, amma duk da haka ba su saki yaron ba.
Bayan samun rahoton, kwamishinan ƴan sanda Ibrahim Bakori ya umarci sashen yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar da su fara amfani da dukkan hanyoyin bincike da na aiki domin gano masu laifin.
Bincike mai zurfi da aka gudanar tare da amfani da fasaha ya kai ga gano maboyar waɗanda ake zargin, inda aka kama su.
Wadanda aka kama sun haɗa da Hassan Umar mai shekara 26, Abdullahi Hamisu mai shekara 19 da kuma Hussaini Saminu mai shekara 24, duk mazauna unguwar Gwammaja a kano.
Bincike ya nuna cewa an tsare yaron a gidan Hussaini Saminu a cikin unguwar Gwammaja, inda daga bisani aka ceto shi ba tare da ya ji rauni ba kuma aka mayar da shi ga iyalansa.
An kuma kwato Naira Dubu 930 daga cikin kuɗin fansa da aka biya.
Kwamishinan ƴan sanda ya yaba wa jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane bisa ƙwarewa da jajircewarsu, tare da godiya ga ofishin babban sufeton ƴan sanda IGP Olatunji Rilwan Disu bisa gudummawar fasaha da ta taimaka wajen nasarar aikin.
Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da garkuwa da mutane da sauran laifuka masu nasaba da tashin hankali, tare da gargadin masu aikata laifi cewa jihar Kano ba za ta zama mafaka gare su ba, sannan ya buƙaci iyaye su kula da ‘ya’yansu tare da sanar da duk wani abu mai kama da shakku ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.









































