Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi nasarar kubutar da wani yaro dan shekara biyu da aka yi garkuwa da shi, tare kuma da kama mutum uku da ake zargi da wani bangare na kudin fansar da aka biya.
Jami’in wulda da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a ranar Asabar.
Kiyawa ya bayyana cewa a ranar 19 ga watan Afrilu, wani mutum dake zaune a unguwar Gwammaja karamar hukumar Dala ya kai rawoton wani da ba a san kowane ne ba yayi garkuwa da dansa mai suna Aliyu Muhammad dan shekaru 2 a kofar gidansu.
Inda ya bayyana cewa mutanan da akezargi su nemi iyayen yaron da su biya kudin fansa Naira miliyan 1, wanda kuma suka biya. Yayin da kuma suka ki sakin yaron duk da biyan kudin fansar.
Bayan da kwamishinan ‘Yan sanda na jihar, CP Ibrahim Bakori ya samu labarin, ya umarci rundunar sashin yaki da masu satar mutane (Anti-Kidnapping) da su yi duk mai yiyuwa wajen kubutar da yaron.
Kiyawa ya kara da cewa bayan gudanar da aiki cikin kwarewa, an yi nasarar kama wadanda ake zargin wanda ya hada da Hassan Umar mai shekaru 26 da Abdullahi Hamisu mai shekaru 19 da kuma Hussaini saminu mai shekaru 24 dukkan nin su ‘yan asalin unguwar ta Gwammaja a jihar ta Kano.
A binciken da ‘yan sanda suka gudanar, sun gano cewa wadanda ake zargin sun boye yaron a gidan Hussaini Saminu a unuwar Gwammaja.
Kiyawa ya kuma tabbatar da kubutar yaron ba tare da wata cutarwa ba, ‘yan sanda kuma su mikashi ga iyalansa. Ya kuma tabbatar da an samu kudi Naira 930,000 daga hannunsu.
Bakuri, ya yaba wa jami’an yaki da masu satar mutane (Anti-Kidnapping) bisa namijin kokarin da suka yi na kubutar da yaron ba tare da samun wani rauni ba, ya kuma gode wa Babban Sifetan ‘yan sanda na kasa, IGP Olatunji Rilwan Disu bisa gudummar da yake baiwa jami’an rundunar a fadin kasa.
Bakori ya kuma tabbatar da cewa baza su saurara ba a yakin da suke da masu garkuwa da mutane, inda yace “masu aikita laifi su shaida jihar Kano bas u da gurbin zama.”
Haka zalika, ya yi kira ga iyaye da su ci gaba da sanya ido akan yaransu, tare da kai rawoton duk wani motsi da basu yarda da shi ba ga ‘yan sanda. Ya kuma yi kira ga sauran jama’a da su ci gaba da baiwa rundunar hadin kai ta hanyar basu sahihan bayanai ta lambobin kiran gaggawa na 08032419754 da 08123821575 da kuma 09029292926.
Daga karshe y ace za a gurfanar da wadanda aka kama din a gaban koto bayan kammala cikakken bincike.












































