Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kaddamar da wani gagarumin a fadin ƙasa domin yaƙi da wulaƙanta takardun Naira da kuma ɓoye su, yayin da ake gab da shiga lokacin bikin ƙarshen shekara.
A wajen taron kaddamarwar da aka gudanar a Abuja, Mataimakin Gwamnan CBN a sashen ayyuka, Bala Bello, wanda Daraktan sashen harkokin Kuɗi da kula da Rassa, Dr. Adetona Adedeji, ya wakilta, ya bukaci al’ummar Najeriya da su sauya dabi’a wajen mu’amala da Naira, yana mai jaddada cewa hadin kai ne kadai zai iya kare martabar kuɗin ƙasa.
Kamfen ɗin, wanda aka yi masa taken “Naira Darajar Mu Ce: Ku Kula Da Ita”, ya yi Allah-wadai da yadda ake wulakanta Naira ta hanyar jefa ta a biki, lanƙwashe ta, tsagawa, rubutu a kanta, da kuma lalata ta.
Bello ya ce irin wannan dabi’u ba wai kawai suna rage darajar kuɗin ƙasa ba ne, har ma suna ƙara tsadar buga sabbin takardun kuɗi.
Karin labari: CBN ya rage kudin rance zuwa kashi 27%
Ya kara da cewa, “Naira ba kawai hanyar biyan kuɗi ba ce., ita alamar darajar ƙasa ce, alamar mulkin kai, da kuma haɗin kanmu a matsayin al’umma, kuma idan aka ci gaba da wulakanta ta, hakan zai rage amincewa da ita a idon jama’a.”
Ya bayyana cewa wannan kamfen ba na Babban Bankin Najeriya kaɗai ba ne, illa dai kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da bankuna, ƙungiyoyin sufuri, ‘yan kasuwa, shugabannin kasuwa, makarantun gwamnati da na addini, kungiyoyin farar hula da kuma kafafen watsa labarai.
Bello ya yi gargadi kan ɓoyewa ko kuma tara kuɗi musamman yayin bukukuwan ƙarshen shekara, yana mai cewa hakan na haifar da matsaloli wajen yaduwar kuɗi da kuma jefa tsarin kudi cikin wahala.
Ya bukaci a rungumi hanyoyin biyan kuɗi na zamani da kuma amfani da kuɗi cikin gaskiya.
Haka nan, Hajiya Hakama Sidi Ali, mai rikon mukamin Daraktar Hulɗa da Jama’a a CBN, ta ce bankin yana da niyyar tabbatar da wadatar sabbin kuɗaɗe masu tsabta bisa ga manufofin takardun Kuɗi masu tsabta da aka tanada a dokar CBN ta shekarar 2007.
Ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su girmama Naira, tana mai cewa: “Alhakin kowanne ɗan ƙasa ne ya kula da Naira da daraja.
Kada a watsa ta a biki, ko rubuta a kanta ko a sayar da ita a hanya.
“Mu duka dole mu zama jakadun takardun kuɗi tsarkakku.”
NAN













































