Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya bayyana dakatarwar da aka yi wa Shugabanni da mataimakan shugabannin kananan hukumomin 18 a Jihar Edo a matsayin haramtacce kuma ba bisa ka’ida ba.
AGF wanda ya zanta da manema labarai a Abuja ranar Alhamis ya jaddada cewa tsige su daga mukaminsa ko kuma dakatar da duk wani zababben jami’in LG a kasar nan ba hakkin ‘yan majalisa ne ba.