Buhari ya musanta mallakar filin da FCTA ta kwace a Abuja

Buhari news 750x430

 

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya musanta rahotannin da ke cewa yana da filin da aka kwace a Maitama 1, Abuja, da gwamnatin birnin tarayya (FCTA) ta ce ba a biya kudin da’a ba.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, Buhari ya ce ba shi da alaka da filin da aka ce an ware wa “Muhammadu Buhari Foundation.”

Ya kara da cewa lokacin da aka gayyace shi da ministocinsa su cike fom din mallakar fili, ya ki karba, yana mai cewa ya riga ya mallaki fili a Abuja.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Kungiyar Muhammadu Buhari Foundation ta kasa biyan kudaden takardar izinin mallaka saboda tsadar da aka sanya mata, wanda hakan ya janyo soke filin.

Garba Shehu ya bukaci jama’a su tabbatar da sahihancin labarai kafin yada su, yana mai jaddada cewa Buhari ba shi da alaka da filin da aka kwace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here