Alhaji Aminu Alhassan Dantata, babban dan kasuwan Najeriya kuma dattijo, ya rasu ya na da shekaru 94 a duniya.
Wani dan uwa ya tabbatar da rasuwarsa ga SolaceBase.
Majiyar ta ce shahararren dan kasuwar nan haifaffen Kano ya rasu ne a wani asibiti da ke Abu Dhabi da misalin karfe 3:00 na dare a agogon Najeriya.
Iyalansa za su sanar da lokacin yi masa jana’izar nan gaba kadan.












































