“Ba za mu biya albashin da NLC ke so ba” —Tinubu

Shugaba, Tinubu dimokuradiyya, biya, albashin, NLC
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa mafi karancin albashin da bai fi karfin gwamnati ba za ta biya. A jawabin shugaban kasar a lokacin...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa mafi karancin albashin da bai fi karfin gwamnati ba za ta biya.

A jawabin shugaban kasar a lokacin bikin ranar Dimokuradiyya ya sanar da Majalisar Dokoki ta kasa cewa nan ba da jimawa ba zai aike mata takardar dokar sabon mafi karancin albashi na kasa.

Daga bisani ya ta yi wani jawabin a daren Larabar a dakin taro na gidan gwamnati da ke Abuja, a lokacin liyafar bikin cika shekaru 25 na ranar dimokuradiyya.

Karin labari: “Za’a ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziƙi duk da wahalhalun da ake fuskanta” – Tinubu

Da yake magana kan batun mafi karancin albashi ga shugabannin majalisar dokokin kasar, wanda shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya wakilta, shugaba Tinubu ya ce gwamnati za ta yi abin da ykamata, amma abin da za ta iya za ta biya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here