Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shiga jerin mutanen da ke kira ga gwamnatin tarayya akan ƙara wa’adin daina karɓar kudaden Naira da aka canjawa fasali (N1000, N500, N200).
Yace ba laifi bane canja fasali kuɗi, kuma ba sabon abu bane ga yan Nigeria, amma wa’adin ranar 31 ga watan Janairu yayi kaɗan, saboda haka ya kamata a kara.












































