An Yi Jana’izar Mutane 48 Da Suka Mutu sakamakon Fashewar Tankar Man Fetur A Niger

mass burial

An yi jana’izar gawarwakin mutane 48 bayan fashewar tankar mai a karamar hukumar Agaie ta jihar Niger.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da tankar mai ta yi karo da wata motar tirela dauke da matafiya da shanu daga Wudil a jihar Kano.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba-Arab wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi, ya kuma tabbatar da cewa an yi jana’izar mutane 48.

A cewarsa, bayan ci gaba da bincike da ceto an sake gano wasu gawarwaki 18 daga cikin gawarwakin 30 da aka ruwaito a baya.
“”Bayan ci gaba da bincike da ceto, hukumar ta gano karin gawarwaki 18 wadanda suka kone kurmus, kuma an yi jana’izar dukkan wadanda suka mutu,” in ji shi.
Baba-Arab ya bayyana hadarin ne a ranar Lahadi a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 12:30 na safe tare da Lapai-Agaie mai nisan kilomita 2 daga unguwar Dendo a Agaie LG.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here