Jami’an ‘yan sandan farin kaya DSS sun kubutar da mahaifiyar dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC AA. Zaura, bayan ta kwashe kimanin sa’o’i 24 a hannun masu garkuwa.
Abaya dai jaridar Solacebase ta ruwaitu cewa masu garkuwa da mutane sun sace mahaifiyar AA. Zaura ne a karamar hukumar Ungogo da ke cikin jihar Kano a ranar Litinin.
Shugaban karamar hukumar Ungogo ya tabbatar wa da jaridar Solacebase cewa an kubutar da ita ne daga hannun masu garkuwa a jihar Jigawa.
Wani jami’in hukumar ta DSS wanda bayaso a bayyana sunan sa, ya ce sun kubutar da Hajiya Laure ne tare da wata tsohowa wadda aka yi garkuwa da ita kwanaki uku da suka wuce.
Ku dakace mu, karin bayani yana nanan gaba.













































