
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kira “ƙasashen da ake damuwa da su” saboda abin da ya kira ci gaba da kisan kiyashin Kiristoci a wasu sassan ƙasar.
Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na Internet a ranar Juma’a, inda ya ce Amurka dole ta tsaya tsayin daka wajen kare ’yancin addini da kuma adawa da zaluntar Kiristoci a ko’ina cikin duniya.
Wannan matakin ya dawo da matsayin da aka fara ba Najeriya a watan Disamba na shekarar 2020 a lokacin mulkinsa, lokacin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta saka Najeriya a cikin ƙasashen da ke take haƙƙin ’yancin addini, bisa dokar ƙasa da ƙasa ta ’yancin addini.
Sai dai gwamnatin shugaba Joe Biden ta cire Najeriya daga wannan jerin a shekarar 2021, abin da ya jawo suka daga ƙungiyoyin addini da kuma wasu ’yan majalisar dokokin Amurka, waɗanda suka ce tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta a Najeriya ya ƙara muni.
Haka kuma, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar yankin West Virginia a Amurka, Riley M. Moore, ya rubuta wa shugaba Trump wasiƙa yana kira ga gwamnatin Amurka da ta sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake damuwa da su saboda abin da ya kira cin zarafi da kisan gilla ga Kiristoci.











































