Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Honarabul Alhassan Ado Doguwa, ya lashe zaben dan Majalisar Tarayya mai wakilatar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada na Jihar Kano.
Tun a shekarar 2007 Honarabul Doguwa ya shiga zauren majalisar, inda a yanzu ya zamana cewa ya lashe zaben kujerar karo na biyar a matsayin mai wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada a matakin Tarayya.












































