Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya bayyana cewa a kullum jami’an tsaro da sojoji suna fuskantar matsin lamba don hada baki dasu a lokutan zabe ta hanyar basu makudan kudade, sai dai ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara amincewa da sojoji a yayin da suke kokarin ganin ba ruwansu da siyasa bisa ga umarnin shugaban kasa.
Da yake jawabi yayin taron tattaunawa na mako-mako a yau, babban hafsan hafsoshin tsaron ya bayyana matakan da sojoji suka dauka wajen yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashi da makami. ya bayyana cewa ana horar da ma’aikata da su bi ka’idojin da aka gindaya na aiki kafin, lokacin da kuma lokacin bayan zabe.
Hukumar tsaron ta kara da cewa sama da mutane dubu 300 ne aka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane tun daga shekarar 2016 yayin da ‘yan gudun hijirar da suka tsere daga arewa maso gabas saboda tada kayar baya suka fara komawa.
Mista lrabor ya amince cewa har yanzu akwai barna da ake tafkawa a cikin sojoji, amma ya ce baza su yi nasara ba. A saboda haka ne ya karyata zargin da wata kafar yada labarai ta kasa da kasa ta yi a baya-bayan nan inda ya zargi sojoji da aiwatar da zubar da ciki sama da dubu 10 ba bisa ka’ida ba kan matan da yakin Arewa maso Gabas ya shafa.
A cewarsa, ba zai taba yiwuwa sojoji su tsunduma cikin shirin zubar da ciki ba tun a shekarar 2013 kuma a matsayinsa na kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole tsakanin 2016 zuwa 2017 bai taba jin wani abu makamancin haka ba.
Don haka ya yi Allah-wadai da rahoton, yana mai nuni da cewa sojoji ba su da masaniyar wasu karin yankunan da ba su da zaman lafiya a kasar.
Ya kara da cewa kokarin da sojoji suke yi wajen yaki da satar danyen mai yana samun sakamako mai kyau inda aka samu karuwar danyen man da ake hakowa ganga miliyan 1 da dubu 600 a kowace rana.













































