Kimanin fursunoni 240 ne suka tsere daga Gidan Ajiya Da Gyaran Hali (MSCC) da ke Kabba a Jihar Kogi, bayan wani hari da har yanzu ba a san ko su waye suka kai ba.
Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali Mista Francis Enobore ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa harin ya faru ne da tsakar dare ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce maharan ɗauke da muggan makamai sun yi ba-ta kashi da masu gadin wajen.
Karanta Wannan: {BIDIYO}:Yadda Aka Ceto Ɗalibai 75 Da Aka yi Garkuwa Da Su A Zamfara
Sanarwar ta kara bayyana cewa Kwanturola – Janar, Haliru Nababa ya ba da umarnin a fara gudanar da bincike domin dawo da wadanda suka tsere nan take. ”
Kwanturola-Janar din ya kuma yi kira ga jama’a da su bai wa jami’an tsaro bayanan sirri da za su taimaka wajen kamo wadanda suka tsere, ” in ji sanarwar.
Karanta Wannan: Al’ajabi: Wani Dalibin Kwalejin Kimiyya Da Kere-Kere Ya Rataye Kansa
An kafa gidan gyaran hali na Kabba wato (MSCC) shekarar 2008 tare da damar dukar fursunoni 200.
Saidai a halin da ake ciki, fursunoni 294 na tsare daga cikin su 224 wadanda ake tsare da su gabanin shari’a da kuma fursunoni 70 da aka yankewa hukunci.













































