Sanatan Kano tsakiya Ibrahim Shekarau a yau Laraba ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP a hukuman ce.
Tun a 29 ga watan Agusta, Shekarau tare da magoya bayan sa suka fice daga jam’iyyar NNPP saboda zargin rashen adalci da akeyi musu a jam’iyyar.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawan, ya karanta wasikar da shekarua ya ake da ita gaban majalisar.
Shekarau a cikin wasikar ya ce shida magoya bayan sa sun fita ne saboda cemma manufar su ta siyasa.
Bayan sanrawar ficewar tasa, sanatocin PDP karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Philip Aduda da kuma shugaban masu tsawatarwa ban garen marasa rinjaye Chukwuka Utazi sun karbe Shekarau.













































