Zamu ci gaba da tallafawa manoma domin bunkasa tattalin arzikin Jihar Jigawa

images
images

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudurinta na inganta harkokin noman alkama a Fadin Jihar.

Mai bawa Gwamnan shawara kan harkokin Noman alkama, Alhaji Yasa’a Wada Abubakar Kiyawa, ne ya bayyana hakan ya yin zantawarsa da Jaridar Solacebase ranar Talata a wani bangare na bikin karrama manoman da suka zama zakarun gwajin dafi a jihohin shiyyar arewa maso yammacin Kasar nan da Kungiyar FMAN ta shirya a Kano.

Yasa’a Wada, yace sakamakon nuna Kwazo da Manoman Alkama a Jihar Jigawa ke nuna wa hakan yasa Gwamnatin Jihar ta dauki ganbaren samar musu da kayayyakin aiki, domin inganta harkokin noman alkamar, kamar yadda Gwamnatin ta tallafi sauran manoma a Jihar.

Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar

Yasa’a Wada Abubakar, ya kara da cewa, Gwamnatin ta yi Alkawarin ci gaba da bada gudunmawa wajen samar da kayan aikin zamani tare da bawa Manoman horo na musamman game da yadda zasu gudanar da harkokin nomansu a zamanance.

Yasa’a ya kuma yi kira ga sauran al’umma dasu rungumi noma a matsayin sana’a domin shi ne kadai hanyar da zata taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here