Jihar Kogi ta tabbatar da ceto shugaban makaranta, jami’in NECO da daliban da aka sace

Usman Ododo 750x430

Gwamnatin Jihar Kogi ta tabbatar da ceto mutum 4 da aka yi garkuwa da su a wani hari da aka kai wata haramtacciyar cibiyar jarrabawa a Olowa, Karamar Hukumar Dekina, yayin da ake gudanar da jarrabawar kasa ta NECO.

Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa, Mr. Kingsley Fanwo ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Lokoja.

Fanwo ya ce an ceto wadanda abin ya shafa ne bayan gudanar da wani aikin ceto mai tsari da Gwamna Ahmed Ododo ya ba da umarni nan take bayan faruwar lamarin.

A cewarsa, gwamnan ya umarci mai bashi shawara kan harkokin tsaro, Cmdr. Jerry Omodara Mai Ritaya, da ya jagoranci hadin gwiwar aikin da ya hada Sojojin Najeriya, Hukumar Tsaro ta DSS, Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa da kungiyoyin ‘yan banga na cikin gida domin tabbatar da sakin wadanda aka yi garkuwar da su.

Ya ce jami’an tsaro sun shiga dajin da ake zaton masu garkuwar sun boye, wanda hakan ya kai ga samun nasarar ceto wadanda abin ya shafa a ranar Alhamis.

Fanwo ya ce yayin da yake duba Motocin Yaki masu Kariya da gwamnatin jihar ta saya kwanan nan, Ododo ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa ana kokari sosai don tabbatar da dawowar wadanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.

“Bayan sa’o’I kadan, wadanda aka yi garkuwa da su sun samu ‘yanci. Matakan da aka dauka na matsa lamba da kuma kewaye dajin da jami’ai dauke da makamai ya sa ‘yan ta’addan suka bar wadanda suka sace suka tsere,” in ji shi.

Ya bayyana sunayen wadanda aka ceto shugaban makaranta, jami’in NECO da dalibai 2, inda ya kara da cewa suna cikin koshin lafiya.

“Suna cikin koshin lafiya kuma a halin yanzu suna tare da hukumomin tsaro don yin tambayoyi da kuma duba lafiya,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce jami’an tsaro har yanzu suna cikin daji don bin diddigin da kama wadanda suka tsere.

“Niyarmu a bayyane take. Duk wanda ya zabi hanyar aikata laifi a Jihar Kogi zai fuskanci cikakken hukuncin doka,” in ji shi.

Fanwo ya yaba wa Sojoji, DSS, ‘Yan Sanda da jami’an tsaro na cikin gida bisa kwarewar da jajircewarsu, inda ya bayyana ceto a matsayin nuni da ingantacciyar hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here