Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da zabar mataimakin sa, Alhaji Murtala Sule Garo, a matsayin abokin takararsa na zaben gwamnan 2027.
Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin.
Gwamna Yusuf ya yi wannan sanarwa ne a yayin wani taro na musamman da masu rike da mukamai a Gwamnatin Tarayya wadanda suka fito daga Jihar Kano, wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano da ke Abuja.
Gwamnan ya ce wannan yanke hukunci ya biyo bayan aminci, jajircewa da kuma kwazo na musamman da Garo ya nuna wajen cigaban Jihar Kano tun bayan da ya hau kan mukamin Mataimakin Gwamna.
Ya bayyana gamsuwarsa da yadda suke aiki tare, yana mai cewa Garo ya nuna kwarewa, jajircewa da kuma daukar nauyin aikin da ya yi.
“Ba ni da nadama kan zabin Garo a matsayin Mataimakin Gwamna a cikin watannin nan, kuma ya tabbatar da cewa shi ne zabin da ya dace. Ina so in tabbatar muku da cewa ina da cikakken kwarin gwiwa a kansa,” in ji Gwamna Yusuf.
Gwamnan ya kuma bayar da cikakken goyon baya ga Mataimakin Gwamnan, inda ya bayyana shi a matsayin abokin aiki wanda za a iya dogaro da shi, wanda gudunmawar sa ta karfafa gwamnatin wajen cimma ci gaba mai amfani ga Jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya kara rokon shugabannin jam’iyya, wadanda aka nada na siyasa da magoya baya da su ci gaba da zama da bada hadin kai da jajircewa yayin da gwamnatin ke ci gaba da karfafa nasarorin da ta samu tare da shirin fuskantar zaben 2027.











































