Gwamnatin Kaduna ta yaba da gurfanar da mutane 24 kan kisan gilla, ta yi gargadi kan daukar doka a hannu

Uba Sani 1 750x430

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi maraba da gurfanar da mutane 24 da ake zargi da hannu a kisan wata mata a Maraban Jos.

Gwamnatin ta bayyana hakan a matsayin wani mataki wajen tabbatar da adalci da kuma tilasta bin doka.

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu, Malam Ahmed Maiyaki ya fitar a ranar Talata.

Maiyaki ya yaba wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna bisa dauki mataki cikin gaggawa da kuma gudanar da bincike mai kyau kan lamarin.

Ya yaba wa kwarewar ‘yan sanda wajen tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Kwamishinan ya ce gwamnatin Gwamna Uba Sani ta yi Allah wadai da dukkan wani nau’in tashin hankali da ayyukan karya doka.

A cewarsa, babu wani mutum ko kungiya da ba hukumomin tsaro da na kotu ba, da ke da ikon daukar doka.

“Doka da oda sune ginshikin kowace al’umma a dimokuraɗiyya,” in ji Maiyaki.

Maiyaki ya kuma bukaci mazauna garin da su bayar da rahoton duk wani zargin ayyukan laifi ga hukumomin tsaro domin a dauki mataki, in da ya yi gargadin cewa duk wanda ya dauki doka a hannu zai fuskanci hukunci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here