Ta’addanci: Kotun ta yanke wa mahaifiya da ‘yar’uwar shahararren dan bindiga hukuncin dauri shekaru 40 kowacce

Terrorism Court sentences DSS arrested mother sister o

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Juma’a ta yanke wa mahaifiya da ‘yar’uwar marigayi shahararren dan bindiga Kachallah Ibrahim Battujo hukuncin dauri shekaru 40 kowacce.

Masu laifin, Safiya Salihu da Halima Abdullahi, kotu ta gano sun bada bayanai ta wayar tarho ga Battujo domin taimaka masa wajen ayyukan ta’addancinsa, laifin da ya saba wa Sashi na 26 na Dokar Hana Ta’addanci ta 2022.

Kotun, a cikin hukuncin da Mai Shari’a Hauwa Yilwa ta yanke, ta kuma yanke wa matan biyu hukunci kan boye bayanai ta hanyar gazawa wajen bayyana ayyukan Battujo ga jami’an tsaro da ‘yan sanda domin sauƙaƙe kama shi.

An tabbatar sun ziyarci sansanin shahararren dan bindigar dake daji, inda suka gan shi da makamai, amma sun gaza bayyana hakan ga hukumomin tsaro.

Mai Shari’a Yilwa ta yanke hukuncin ne bayan wadanda ake tuhuma sun amince da laifi kan kara ta 2, 4 da 5 daga cikin tuhuma biyar masu alaka da ta’addanci da Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya shigar.

Sai dai, kotun ta sallami tuhuma 1 da 3, wadanda ke zargin sun karbi Naira 490,300 daga Battujo bayan sun san kudin ta’addanci ne.

Kotun ta kuma sallami tuhumar da ta ce sun samu tallafin tafiyar aikin Hajji daga shugaban yan bindigar.

A cewar mai gabatar da kara, ya kamata masu laifin sun san kudin da aka yi amfani da su wajen tafiyar Hajji na ta’addanci ne, don haka sun aikata laifin da ya saba wa Sashi na 21 na Dokar Hana Ta’addanci ta 2022 wanda ya saba da doka.

Darakta mai gabatar da kara na Tarayya, Barr. Rotimi Oyedepo, SAN ya roki kotun ta soke tuhume-tuhume biyun, sannan ya nemi kotun ta yanke wa wadanda ake tuhuma hukunci kan sauran tuhume-tuhume uku.

Jami’an tsaro sun kashe fitaccen dan bindiga Battujo a ranar 10 ga Yunin 2026, a daji kusa da Iluke a Karamar Hukumar Kabba/Bunu ta Jihar Kogi.

“Cewa, Halima Abdullahi da Safiya Salihu, mata, manya, na Dungun Mu’aza, Karamar Hukumar Sabuwa, Jihar Katsina, a wani lokaci a shekarar 2026, a Jihar Katsina, a cikin ikon wannan Kotun Mai Daraja, kun aikata laifi lokacin da kuka taimaka wa ayyukan Battujo, shahararren shugaban yan bindiga, ta hanyar bada bayanai ta wayar tarho zuwa ga Battujo, laifin da ya saba doka kuma ana iya hukunci a kan shi dogaro da Sashi na 26 na Dokar Hana Ta’addanci ta 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here