2027: ADC Tsagin Bashir ya zabi Kachikwu a matsayin dan takarar shugaban kasa

Dumebi Kachikwu 750x430

Wani bangare na jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Abdulkadir Bashir ya zabi Dumebi Kachikwu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), ya ruwaito cewa an zabi Kachikwu a ranar Lahadi a wani taro na musamman na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.

Zabensa ya biyo bayan kuri’ar murya da wakilai daga jihohi 36 na kasar da Babban Birnin Tarayya suka bayar.

A jawabinsa na karbar takara, Kachikwu ya yi alkswarin sadaukar da kansa wajen gina Najeriya ta hanyar mulki da zai hada kai da gyare-gyare.

Kachikwu ya ce wasu ‘yan siyasa sun raina talakawa kuma sun yi kokarin kwace tsarin jam’iyyar domin moriyar kansu da burinsu na siyasa.

“Talakawa ne kashin bayan dimokuradiyyarmu, kuma saboda su ne nake karbar wannan takara da alfahari,” inji Kachikwu.

Ya gode wa shugabannin jam’iyyar, mambobi, shugabannin a jihohi, Kwamitin Gudanarwa na Kasa, da iyalinsa bisa tallafawa burinsa na siyasa da sadaukarwarsa ga ci gaban kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here