Sabon Mataimakin Gwamnan Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya fara aiki a hukumance, inda ya yi alkawarin tabbatar da samar da ci gaba da bunkasar jihar.
SolaceBase ta ruwaito cewa Garo ya isa ofishinsa da safiyar Laraba, tare da manyan jiga-jigan APC, ciki har da tsoffin gwamnoni Mallam Ibrahim Shekarau da Abdullahi Umar Ganduje, da sauran manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.
A cikin sakonnin taya murna daban-daban, Shekarau da Ganduje sun taya sabon mataimakin gwamnan murna tare da karfafa shi da ya ci gaba da mai da hankali, sadaukarwa da jajircewa ga manufar ci gaban jihar Kano.
Sun jaddada muhimmancin biyayya, ladabi da aiki tare wajen tabbatar da nasarar gwamnatin yanzu.
A nasa jawabin, Garo ya nuna jin dadinsa matuka kan goyon baya da hadin kai da shugabannin APC da masu ruwa da tsaki suka nuna masa.
Haka zalika, ya kuma gode wa Shekarau da Ganduje kan jagorancinsu, yana mai yin alkawarin ci gaba da neman shawararsu wajen gudanar da ayyukansa.
Mataimakin gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, kan ganin ya cancanci wannan mukami.
Garo ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa zai yi aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba wajen mara wa gwamnati baya domin cika alkawuran da ta yi.
Haka kuma, ya sake jaddada aniyar sa na “Kano First Agenda”, yana mai cewa mayar da hankalinsa zai kasance kan manufofi da shirye-shiryen da za su habaka ci gaba da walwalar jihar baki daya.










































