Rundunar sojin Nijeriya a ranar Juma’a ta kafa kotun soji ta musamman da zata binciki sojojin da ake zargi da kitsa juyin mulki, wanda ta fara aiki bisa doka.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), ya rawaito an kai jami’an da ake zargi zuwa wurin da aka tanadarwa kotun Guards Brigade Scorpion, Asokoro, da misalin karfe 8:53 da rakiyar jami’ai.
An hana ‘yan jarida shiga wurin da ake gudanar da zaman, yayin da zaman ke gudana cikin sirri.
Lauyoyi masu zaman kansu da dama sun halarci wurin da ake zaman, inda suka bukatar a baiwa wadanda ake zargin damar kawo masu kare su a yayin zaman.
Zaman da kotun sojin ta fara ya nuna cewa an fara zama domin fara shari’ar bayan daukar watanni ana gudanar da bincike kan shirin juyin mulkin.
An dai zargi sojojin su 16 da kitsa juyin mulkin a watan Oktoban shekarar 2025 da ta gabata. Cikin sojojin da ake zargi akwai manyan sojoji da kuma kanana, wadanda ake zargi da rashin da’a.
NAN ya rawaito cewa an kawo mutum sama da 30 da ake zargi a mota luxurious kirar Marcopolo.
A wani bangaren, gwamnatin tarayya ta gurfanar da wasu mutane da tsofaffin jami’an sojoji a gaban Babbar kotun tarayya dake Abuja da zargin kitsa juyin mulki.
Cikin wadanda ake zargin akwai wani Manjo Ganaral mai ritaya da ‘yan sanda, wadanda ake zargi da cin amanar kasa da kuma ta’addanci, wanda duk suka ki amincewa da zargin. Inda daga nan kotun ta bukaci a ci gaba da rike so ba tare da bada belin su ba.













































