Kwana guda bayan sace mutane Bakwai daga iyali guda da wasu mutum uku mazauna Unguwar Sabon-Titi da ke Katari a jihar Kaduna, ‘yan bindiga sun sake kai hari inda suka sace wasu ‘yan gida guda a kauyen Kurmin-Uwa kusa da Janjala a karamar hukumar Kagarko ta jihar.
Wani mazaunin garin Kagarko, Ibrahim Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, inda ya ce harin ya faru da misalin karfe 10:23 na dare a ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa da isowar ‘yan bindigar, sun nufi gidan da suka yi niyya kai tsaye inda suka yi awon gaba da mutane bakwai.
Ya lissafo sunayen wadanda aka sace, wadanda suka hada da uwa da ‘ya’yanta shida, da suka hada da Ladi Malachy, Patience Malachy, Promise Malachy, Inama Malachy, Peter Malachy da Aboyi Malachy.
Wani jagoran al’umma da ya nemi a sakaya sunansa ya kuma tabbatar da faruwar sacewar, inda ya ce ya sanar da jami’an tsaro bayan samun labarin harin da aka kai kauyen, wanda ke da nisan kilomita biyu daga garin Kagarko.
Ya bayyana cewa har yanzu ba a samu wata hanyar tuntubar ‘yan bindigar ba, yana mai nuna damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da faruwa a kauyuka da dama a karkashin karamar hukumar Kagarko.
Wani jami’in tsaro ya ce zai bincika lamarin tare da bayar da karin bayani daga baya, yana mai cewa suna cikin daji tun ranar Talata suna kokarin gano maboyar ‘yan bindigar domin ceto wadanda aka sace a Katari a ranar Laraba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Hassan Mansur, bai amsa kiran waya ko sakon da aka tura masa ba dangane da sabon harin sace mutanen.












































