Adelabu ya musanta yin murabus daga mukamin ministan lantarki

Chief Adebayo Adelabu

Ministan lantarki, Adebayo Adelabu, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi murabus daga mukaminsa, yana mai bayyana irin wadannan labarai a matsayin karya da yaudara a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan makomarsa ta siyasa.

Wannan martani ya zo ne a lokacin da ake fuskantar rashin tabbas sakamakon umarnin gwamnatin tarayya da ke bukatar dukkan masu rike da mukaman siyasa da ke da burin tsayawa takara a zaben 2027 su sauka daga mukamansu.

Da yake mayar da martani ta wata hira ta WhatsApp da manema labarai a ranar Talata, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Bolaji Tunji, ya karyata rahotannin, yana mai jaddada cewa ministan na ci gaba da gudanar da aikinsa yadda ya kamata a bangaren lantarki.

Ya kuma bayyana hotunan wasikar murabus din da ake yadawa tare da lakabin “labarin karya,” domin nuna cewa babu gaskiya a ciki.

Rahotanni sun nuna cewa jita-jitar ta karade ne bayan wasu kalamai da ministan ya yi a baya, wadanda wasu suka fassara a matsayin alamun cewa zai iya shiga siyasa.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a makon da ya gabata, Adelabu bai tabbatar da ko zai yi murabus ba, duk da cewa ya amince da cewa akwai wa’adin yanke shawara kan batun siyasa kafin zaben 2027.

Ya kuma jaddada cewa magance matsalolin lantarki a Najeriya shi ne babban abin da ya sa a gaba a halin yanzu, yana mai cewa har yanzu yana mai da hankali kan aikin da yake yi, duk da yiwuwar yanke hukunci kan makomarsa nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here