Wata Matar aure ta yanke al’aurar mijinta a jihar Yobe

AI generated image of a young lady 750x430

Wata matar aure mai shekaru 18 a Potiskum ta jihar Yobe, wadda ba a bayyana sunanta ba, ana zarginta da yanke al’aurar mijinta a wani mummunan lamari da ya girgiza al’umma a yankin.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na dare ranar 6 ga Fabrairu.

Sanarwar ta nuna cewa an kai rahoton lamarin ofishin ’yan sandan Potiskum da misalin karfe 3 na rana a ranar da lamarin ya faru, bayan matar ta tsere daga wurin da aka aikata laifin.

Rundunar ’yan sandan ta ce matar, wadda ke tsere a halin yanzu, ta yi amfani da wuka mai kaifi wajen raunata mijinta kafin ta gudu, abin da ya jawo mummunan rauni ga wanda abin ya shafa.

Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin tare da kai mutumin zuwa asibitin kwararru na jihar Yobe da ke Potiskum domin samun agajin gaggawa, daga nan aka tura shi zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Azare inda yake samun kulawa.

Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin cafke wadda ake zargi da kuma gano ainihin abin da ya jawo aikata laifin, tare da bayyana cewa ba za a fitar da wasu muhimman bayanai ba domin kare mutumin daga ƙarin raɗaɗi.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya yi Allah wadai da lamarin, yana mai cewa aure ya kamata ya kasance bisa girmamawa da fahimta da hakuri, ba tare da tashin hankali ko cin zarafi ba.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here