Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai fara ziyarar ƙasa ta kwanaki biyu zuwa ƙasar Birtaniya bayan gayyata a hukumance daga Sarkin ƙasar Birtaniya Charles na uku, lamarin da ya zama ziyarar ƙasa ta farko da wani shugaban Nijeriya zai kai ƙasar cikin tsawon shekaru 37.
Sanarwar ziyarar ta fito ne a wata sanarwar da shafin iyalan masarautar Burtaniya suka a hukumance, inda aka bayyana cewa Sarkin ƙasar Birtaniya Charles na uku da Sarauniya Camilla za su karɓi bakuncin shugaban ƙasar Najeriya a fadar Windsor.
An kuma bayyana cewa shugaban ƙasar zai samu rakiyar matarsa Uwargidan shugaban ƙasa Oluremi Tinubu a yayin ziyarar, inda za a gudanar da muhimman tarurruka na diflomasiyya da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya bayyana cewa wannan ziyarar ita ce ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai Birtaniya a matsayin ziyarar ƙasa tun bayan shekaru 37 da suka gabata.
Ya jaddada cewa shugaban ƙasa Tinubu da Uwargidan shugaban ƙasa Oluremi Tinubu za su samu karɓa ta musamman daga Sarkin ƙasar Birtaniya Charles na uku da Sarauniya Camilla, abin da ke nuna muhimmancin dangantakar siyasa da diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Ziyarar ƙarshe ta irin wannan matsayi daga Najeriya zuwa Birtaniya ta faru ne a zamanin tsohon shugaban mulkin soja Ibrahim Babangida, wanda marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu ta karɓa a fadar sarauta na tsawon kwanaki huɗu.
Rahoton ya kuma nuna cewa shugaba Tinubu da Sarkin ƙasar Birtaniya Charles na uku sun taɓa haɗuwa a lokuta daban-daban tun bayan da dukkansu suka hau muƙamansu, ciki har da ganawarsu a Dubai da kuma wata ganawa ta musamman da aka yi a fadar Buckingham, tare da nuna irin tsohuwar alaƙar da Sarkin ke da ita da Najeriya da kuma sha’awarsa ga al’adun ƙasar.













































