Kamar guguwar da ta taso a hedikwatar jam’iyyar APC ta lafa bayan da juyin mulkin da aka shirya wa shugaban kwamitin rikon kwarya Gwamna Mai Mala Buni, ya ci tura.
Wannan al’amari ya bayyana ne bayan rashin halartar gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello da kuma bayyanar Sanata John James Akpanudoedehe, sakataren kwamitin, wanda nan take bayan ya ci gaba da aiki a ranar Talata, ya fitar da sanarwar manema labarai.
Yadda Sakataren APC Sanata John James Akpanudoedehe ya isa hedikwatar jam’iyyara yau Talata
Gwamna Abubakar Sani Bello ne ke jagorantar al’amura a hedikwatar jam’iyyar tun ranar Litinin da ta gabata tare da goyon bayan Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
El-Rufai a wata hira da yayi kwanan nan ya ce Mai Mala Buni da ke jinya zai dawo kasar ne kawai a matsayin gwamnan jihar Yobe, ba a matsayin shugaban jam’iyyar ba.
Har ila yau, Sakataren kwamitin Sanatan wanda a cikin rudani a jam’iyyar ya ce ya yi murabus duk da cewa ya musanta labarin bayan da da ya sake kunno kai a hedikwatar jam’iyyar a ranar Talata.
Sai dai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gaza amincewa da shugabancin Abubakar Sani Bello, lamarin da ya tilasta masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC janye matakin da suka dauka.
A halin da ake ciki kuma, jam’iyyar ta shirya wata tawagar manyan lauyoyi domin yin bayani kan wani umarnin kotu na dakatar da babban taron jam’iyyar APC na kasa. Don haka muna kira ga Hukumar Shari’a da ta ba wa wannan al’amari kulawar da ya dace a yunkurinmu na ficewa daga umurnin kotu da kuma ba da damar gudanar da babban taron kasa na gaskiya da adalci wanda ya cancanci babbar jam’iyyar mu ta APC.













































