Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a makon farko na watan Janairu.
Wannan mataki na nufin kawo ƙarshen kusan shekaru arba’in na alaƙar siyasa tsakaninsa da Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya kasance mai ba shi gata da jagoranci a siyasance.
Ficewar Gwamna Yusuf daga NNPP za ta sa jam’iyyar ta rasa dukkan gwamnonin da take da su a Najeriya, kasancewar shi kaɗai ne gwamna daga jam’iyyar.
A lokaci guda kuma, ana sa ran gwamnan zai shiga shirye-shiryen tarukan APC da aka tsara yi a watan Fabrairu domin karɓar cikakken iko da jam’iyyar a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya fara neman goyon bayan ’yan majalisar tarayya, majalisar dokokin jihar da shugabannin ƙananan hukumomi domin ƙarfafa matsayinsa a sabon tafarkin siyasar.
Sai dai yawancin ’yan majalisar dokokin jihar daga NNPP sun amince da shirin ficewar gwamnan, ciki har da shugaban majalisar, lamarin da ke ƙara masa ƙarfi a cikin tsarin siyasar jihar.
A yayin da shirin ficewar ke ƙara ɗaukar hankali, Rabiu Musa Kwankwaso ya kira taro da ’yan majalisar dokokin jihar a gidansa da ke Miller Road, inda aka tattauna halin da ake ciki.
DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa a yayin ganawar Kwankwaso ya shaida musu cewa da alama gwamnan yana shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP ya koma APC, saboda haka duk dan majalisar da ya zabi tafiya da gwamna to yana da ikon yin hakan.
Wata majiya ta bayyana cewa, bayan taron, ’yan majalisar sun nemi ganawa da gwamnan domin tattaunawa, amma aka sanar da su cewa matakin komawa APC ya riga ya kammala kuma ba zai sauya ba.
A wani ɓangare, ana hasashen cewa mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdulsalam na iya zama wanda zai fara fuskantar sakamakon rikicin siyasar, domin ana zargin akwai shirin sauya shi da Murtala Sule-Garo domin jawo goyon bayan manyan APC a Kano, yayin da ake tunanin Nasiru Gawuna zai nemi kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a zaɓen 2027.
Tun bayan hukuncin Kotun Ƙoli kan zaɓen gwamnan Kano, gwamnan ya fara yunƙurin shawo kan Kwankwaso da ya koma APC, amma hakan bai samu ba.
A baya, an sha samun kira daga cikin jam’iyyar da wajen ta da ke neman gwamnan ya tsaya da ƙafarsa a siyasance, lamarin da ya ƙara tsananta rabuwar kai a NNPP a Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shugabannin NNPP a ƙaramar hukumar Rogo sun bukaci Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf su yi la’akari da komawa APC domin amfanin siyasar Kano da magoya bayan Kwankwasiyya.
Duk da wannan kira, shugabannin sun jaddada biyayyarsu ga Kwankwaso tare da kira ga haɗin kai, ladabi da girmamawa yayin da ake fuskantar sabon yanayin siyasar jihar.












































