Da ɗumi-ɗumi: Ɗaliban makaranta 130 da aka sace a jihar Neja sun shaƙi iskar ƴanci

school 1 750x429

Dukkan ɗaliban makaranta da aka sace daga makarantar St Mary’s Catholic School da ke yankin Papiri a jihar Neja yanzu sun shaƙi iskar ‘yanci, bayan sakin rukuni na ƙarshe guda ɗari da talatin, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka ceto zuwa ɗari biyu da talatin gaba ɗaya.

Jami’ai daga ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro na ƙasa sun tabbatar da wannan ga ‘yan jarida a ranar Lahadi.

Wannan ci gaban ya kawo ƙarshen kwanaki na damuwa da tashin hankali ga iyalan ɗaliban, tare da nuna gagarumin nasara ga hukumomin tsaro da suka shiga aikin ceto.

An sace yaran ne lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari makarantar kwana, abin da ya haifar da fushin jama’a a faɗin ƙasa da kuma sake tayar da damuwa kan tsaron makarantu a Najeriya.

Mahukunta sun bayyana cewa samun nasarar sakin dukkan waɗanda abin ya shafa ya biyo bayan matsin lambar tsaro mai ɗorewa da haɗin gwiwar da aka yi tsakanin hukumomi, yayin da ake ƙara kira da a ƙarfafa kariyar makarantu tare da ɗaukar matakan gaggawa domin hana maimaituwar irin wannan hare-hare.

 

Cikakken labarin na nan tafe…

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here